Kamfanin NNPCL ba zai taɓa ha’intar Najeriya ba – Mele Kyari

0
31
Kamfanin NNPCL ba zai taɓa ha'intar Najeriya ba - Mele Kyari

Kamfanin NNPCL ba zai taɓa ha’intar Najeriya ba – Mele Kyari

Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPCL, Mele Kyari ya ce babu ruwan jami’an kamfanin a shigar da man fetur da dangoginsa marar kyau cikin ƙasar.

Kyari ya faɗi hakan ne a yayin da yake bayani a ranar Laraba a Abuja a gaban wani kwamitin Majalisar Dattijai ƙarƙashin jagorancin Sanata Opeyemi Bamidele kan zargin da ake yi cewa ana yi wa fannin man fetur ɗin ƙasar zagon ƙasa.

Kyari ya ce a matsayinsa na shugaban kamfanin NNPCL, ya fuskanci hare-haren da ba su dace ba daga kafafen yada labarai daga mutanen da ke yin duk abin da zai haifar da tunanin cewa NNPCL na yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.

KU KUMA KARANTA: Ƙaramin Ministan Man Fetur na neman sasanta NNPC da Ɗangote

Ya ce, kamfanin ba zai taɓa ha’intar Najeriya ba kuma ba zai yi ƙarya ba.

“Mu ba masu aikata miyagun laifuka ba ne kuma mu ba ɓarayi ba ne. Dole mu kare martabarmu don mu yi wa ƙasar nan hidima,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa masana’antar man fetur da iskar gas tana tafka asara kuma akwai abubuwan da ya sani amma ba zai iya magana a kansu ba a bainar jama’a har sai “lokacin yin hakan ya yi”.

Kyari ya nemi a watsa zaman kwamitin a talabijin kai tsaye a nan gaba don ‘yan Najeriya su shaida me yake faruwa.