Kakakin majalisar wakilai ya naɗa Injiniya Usman a matsayin mataimaki na musamman
Daga Idris Umar, Zariya
Kakakin Majalisar Wakilai, Honorabul Tajudeen Abbas, GCON, ya naɗa tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Sabon Gari, Injiniya Muhammad Ibrahim Usman, a matsayin Babban Mai Taimaka Masa kan sha’anin Dokoki.
An tabbatar da naɗin ne a cikin wata sanarwa da aka aika wa tsohon shugaban ƙaramar hukumar.
KU KUMA KARANTA:Kakakin majalisar wakilai ya naɗa Injiniya Usman a matsayin mataimaki na musamman
Bayan sanarwar, sakonnin taya murna sun cika a kafafen sada zumunta, inda ‘yan uwa, abokai da masoya ke murnar wannan naɗin inda suka bayyana a matsayin wanda ya dace da cancanta.
Injiniya Usman, wanda aka san shi da jajircewa da gudummawa wajen ci gaban al’umma a lokacin da yake shugabantar ƙaramar hukumar Sabon Garin, ana sa ran zai yi amfani da ƙwarewarsa da gogewarsa a sabon muƙaminsa a Majalisar Tarayya.