Ka ajiye Kwankwasiyya kafin ka shigo APC – Shugaban Jam’iyar APC a Kano

0
122
Ka ajiye Kwankwasiyya kafin ka shigo APC - Shugaban Jam'iyar APC a Kano

Ka ajiye Kwankwasiyya kafin ka shigo APC – Shugaban Jam’iyar APC a Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Shugaban jam’iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas ya yi kira ga jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da kar ya shigo APC da kungiyar siyasar sa mai suna Kwankwasiyya.

A kwanan nan akwai raɗe-radin mai karfi cewa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, na shirin sauya sheka zuwa APC.

Sai dai kuma da ya ke taron manema labarai a sakatariyar APC ta Kano a yau Juma’a, Abbas ya ce ba ruwan APC da wata ƙungiya ta siyasa cikin jam’iyyar.

Duk da cewa Hon Abbas bai fadi Kwankwasiyya ba, amma a jawabin nasa ya nuna cewa babu wata kungiya da za ta dake da jam’iyyar siyasa da za a bari ta shigo cikin APC.

Ya kara da cewa duk masu tururuwar dawowa APC ba za a ki karbar su ba amma sai sun je mazabu su sun yi rijista.

Ya kuma ce dukkanin shugabannin da ke rike shugabancin jam’iyyar a matakai daban-daban a jihar suna nan akan mukaman su.

Leave a Reply