June 12: Tinubu zai yi wa ƴan ƙasa jawabi gobe

0
54
June 12: Tinubu zai yi wa ƴan ƙasa jawabi gobe

June 12: Tinubu zai yi wa ƴan ƙasa jawabi gobe

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaban kasa Bola Tinubu zai yi jawabi ga kasa da misalin karfe 7 na safe ranar Alhamis a matsayin wani bangare na bukukuwan ranar Dimokuraɗiyya ta shekarar 2025.

Tinubu zai kuma halarci zaman hadin gwiwa na Majalisar Tarayya.

Kwamitin bikin ranar dimokuraɗiyya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

KU KUMA KARANTA: Jawabin mataimakin shugaban ƙasa a taron ranar ‘yansanda ta ƙasa a Abuja

Abdulhakeem Adeoye, wanda ya fitar da sanarwar a madadin Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na kwamitin, ya ce bayan jawabin da shugaban kasa zai yi, zai halarci zaman hadin gwiwa na Majalisar Tarayya da misalin karfe 12 na rana.

Sai dai, a cewar Adeoye, ba za a gudanar da bikin faretin Ranar Dimokuraɗiyya ba. Daga bisani a ranar, za a gudanar da muhawara ta musamman dangane da bikin ranar Dimokuraɗiyya a Dakin Taro na Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja da misalin karfe 4 na yamma.

Taken wannan muhawara shi ne: “Ƙarfafa Nasarorin Dimokuraɗiyyar Najeriya: Bukatar Sauye-sauye masu Dorewa.”

Leave a Reply