Jirgin ƙasan Abuja – Kaduna zai koma aiki a cikin Nuwamba

0
462

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a dawo da zirga-zirgar jiragen ƙasa na Abuja zuwa Kaduna a wannan watan na Nuwamba da muke ciki.

Ministan sufuri na ƙasar Mu’azu Sambo ne ya sanar da hakan a yau Litinin a yayin da yake faɗar nasarorin ma’aikatarsa a Abuja.

A ranar 28 ga watan Maris din 2022 ne aka dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasan Abuja zuwa Kadunan, bayan da ƴan bindiga suka kai wa jirgin hari suka kashe mutum 10 tare da sace wasu da dama.

Ministan ya ce an ɗauki tsauraran matakan tsaro don kare rayuwan fasinjoji kafin sanar da dawowar zirga-zirgar jiragen, sai dai bai faɗi taƙamaimai ranar da jiragen za su fara aikin ba.

Ministan ya ce ma’aikatar tasa ta koyi ɗumbin darasi daga harin da aka kai na watan Maris din da ya janyo dakatar da sufurin.

Leave a Reply