Jawabin mataimakin shugaban ƙasa a taron ranar ‘yansanda ta ƙasa a Abuja

0
121
Jawabin mataimakin shugaban ƙasa a taron ranar 'yansanda ta ƙasa a Abuja

Jawabin mataimakin shugaban ƙasa a taron ranar ‘yansanda ta ƙasa a Abuja

Daga Idris Umar, Zariya

A Taron Kafa Ranar ‘Yan Sanda ta Kasa 7 ga Afrilu, 2025 An gudanar da bikin Ranar Kafa ‘Yan Sanda ta ƙasa na farko a yau a filin Eagle Square da ke Abuja, wanda ya kammala jerin abubuwan da aka gudanar a cikin makon murnar bikin ‘Yan Sanda na shekarar 2025.

Wakilin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan taron, Kashim Shatima ya tabbatar da ƙudurin gwamnatin shugaba Tinubu na samar da Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya da za ta kasance tana da horo mai kyau, kayan aiki na zamani, da kuma kwazo domin yaki da laifuka yadda ya kamata a fadin kasar.

KU KUMA KARANTA:APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Kashim Shettima a zaɓen 2027

A yayin isar da saƙon Shugaban ƙasa, mataimakin ya jaddada cewa wannan mataki na gwamnati yana cikin ƙoƙarin tabbatar da cewa rundunar tsaron ƙasar tana da kayan aiki da fasaha na zamani, kuma suna ci gaba da kasancewa “a gaba a kowane mataki” kan waɗanda ke barazanar ga zaman lafiya, walwala, da ci gaban Najeriya.

A cikin wani mataki na tarihi,ya sanar da ƙaddamar da 7 ga Afrilu a matsayin Ranar Kafa Rundunar ‘Yan Sanda ta ƙasa, ranar da za ta kasance domin girmama shuhadawan ‘Yan Sanda da kuma yabawa kan nasarorin da ma’aikatan tsaron ke samu.

Ranar Kafa ‘Yan Sanda ta ƙasa za ta zama wata ranar tunawa da sadaukarwar da ‘Yan Sanda ke yi wajen tsare rayukan ‘yan Najeriya da kuma girmama jajircewar su wajen tabbatar da tsaro a cikin kasar.

Taron ya sami halarci manyan jami’an gwamnati, wakilan rundunar tsaro, da kuma al’ummar kasar kuma duk sun hadune a wajen don yabawa da fahimtar muhimmancin rundunar ‘Yan Sanda wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.

Leave a Reply