Jarumar Kannywood Dawayya ta buɗe katafaren kantin sayar da kayayyaki a Kano

5
707

Daga Saleh INUWA, Kano

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, furodusa kuma darakta Rukayya da akafi sani da Dawayya ta buɗe wani katafaren kantin sayar da kayayyaki a Kano. Wannan na daga cikin ƙudurinta na faɗaɗa Kasuwancinta.

Ruqayya Dawayya

A wani ɓangare kuma, Ruƙayya Dawayya tana shiga harkokin siyasa, da yin fina-finai, da kuma ayyukan jin ƙai a jihohi Kano, Jigawa da Katsina.

A tarihinta, Dawayya ta taso ne daga ƙasar Saudiyya, inda iyayenta suka kwashe sama da shekara 20, zuwa Kano domin shiga Kannywood. Ta taɓa aure kimanin shekaru takwas da suka gabata, da wani ɗan kasuwan Yola wanda yanzu haka ya kasance mai hasashen filaye a Abuja.

Dawayya with her son Arafat

Sai dai kuma, bayan shekara biyu auren ya mutu, kuma Allah Ya albarkaci auren da yaro ɗaya, mai suna Arafat. Ta haife shi ne a lokacin Arafat a Saudiyya.

Dawayya ta daɗe tana samun nasara a masana’antar inda ta kafa fina-finanta na Dawayya multimedia, sannan ta shirya fina-finai da dama wanda da suka yi suna da nasara. Bata tsaya anan ba, ta haɗa yin fim da wasu sana’o’i kamar sayar da software da kayan kwalliya.

Akwai sanda jaruma Dawayya ta koma Katsina a taƙaice domin ta tsaya takarar ‘yar majalisa, amma hakan bai cimma ruwa ba. Sai ta koma Kannywood da sauri ta ci gaba da shirya fina-finanta.

Jaruma Ruƙayya ta kasance tana haɗa kasuwancinta, tare da aiwatar da ayyukanKwangilada ayyukan jin ƙai. Rukayya Dawayya za ta daura aure da Daraktan hukumar tace fina-finai na jihar Kano, Isma’il Na Abba Afakallah.

Hotunansu na kafin aure da katunan aure sun fito amma mutane kaɗan aka gayyata bikin auren, ta yadda kafafen sada zumunta ba za su yi zaƙe ba, balle har su ƙara gishiri da mai.

Ismail Na Abba Afakallah, da abokansa, da abokan Rukayya Dawayya ne suka halarci bikin buɗe boutique ɗinta da kantin sayar da kayayyaki.

A taƙaice ta yi addu’ar Allah ya sakawa wannan sana’ar albarka, sannan ta yi fatan ƙawayenta suma su kafa sana’o’i nan da can domin a lokacin da suka yi aure, za su iya yin ritaya daga fim, su mayar da hankali kan kula da auren su, da kuma kula da iyalinsu.

5 COMMENTS

Leave a Reply