Jami’o’in Birtaniya za su fara ɗaukar masu sakamakon jarabawar NECO

0
56

Jami’o’in Birtaniya za su fara ɗaukar masu sakamakon jarabawar NECO

Jami’o’in ƙasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO.

Shugaban hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya ce Jami’ar Lead da Jami’ar Birmingham City da ke kasar Birtaniya sun tuntubi hukumar  kan jarabawar da take shiryawa.

Ya ce  jami’o’in sun fara tunanin bai wa daliban Najeriya gurbin karatu da sakamakon jarabawarsu ta NECO.

KU KUMA KARANTA: JAMB zata duba yiwuwar amfani da wayoyin hanu a jarabawar UTME

A fahimtarsa, hakan na nuni da  amincewa da ingancin sakamakon jarabawar NECO ne a idanun manyan jami’o’in ciki da wajen Najeriya.

Farfesa Wushishi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ’yan jarida a Abuja ranar Laraba.

Ya ce NECO ta cika sharudan Jami’ar Birmingham City, kuma a halin yanzu suna aiki tukuru kan ganin sun sami cika sharudan jami’ar Lead.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here