Jami’an tsaro Sun Rufe iya kokin shiga gidan galadiman Kano
Daga Shafaatu Dauda Kano
An wayi gari da ganin jami’an tsaro a harabar gidan Galadiman Kano da ke unguwar Galadanci a karamar hukumar Gwale.
Rahotanni sun bayyana cewa tun cikin daren jiya Alhamis aka hangi jami’an yansanda sun rufe iyakokin gidan na Galadima.
KU KUMA KARANTA:Kwankwaso da Ganduje ku haƙura da rikicin siyasar nan haka domin ci gaban Kano – Kashim Shettima
Wannan na zuwa ne bayan da ake sa ran Sarkin Kano Muhammad Sunusi || zai raka Galadiman Kano, Mannir Sunusi, bayan na dashi kamar yadda al’adar masarautar Kano ta ke.