Iyayen yara sun nemi ɗaukin Gwamnatin Kano akan Makarantar Sakandiren Kwakwaci da ta lalace
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Makarantar sakandire ta kwakwaci, guda ce daga cikin manyan makarantu a yankin karamar hukumar Fagge.
Bayan koken iyayen yaran wannan yankin, wakilin Jaridar Neptune Prime a Kano, ya je wannan makaranta, sai dai wannan makaranta na cikin mawuyacin hali yanzu haka.
Makarantar ta zama mafakar ɓata gari, wanda suke shiga suke aikata shaye-shaye, da harkar sayar da kayan maye.
KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Kano ta rufe wasu rumfuna
Wasu kuma suna shiga suna kashi a ciki, al’ummar wannan yanki da iyayen dalibai sunyi kira ga Gwamnatin Kano da ta kai agajin gaggawa wannan makaranta,
Domin wajen na barazana ga tarbiyya yara, a gefe guda kuma suna bukatar gyara azuzun domin yara su sami isasshen muhalin karatu.