An fafata tsakanin ISWAP da mayaƙan Boko Haram

0
507

Daga Saleh INUWA Kano


Kungiyar ISWAP mai da’awar jihadi a Yammacin Afirka, ta kashe masu yaƙan Boko Haram guda takwas a wata karawa da suka ka yi a Jihar Borno.

Zagazola Makama, wani ƙwararren Manazarci kan Yaƙi da Tayar da ƙayar baya, kuma mai fashin baƙi kan sha’anin tsaro a yankin Tafkin Chadi, ya ce lamarin ya faru ne a garin Jilli da ke tsakanin ƙananan Hukumomin Gubio da Magumeri na Jihar Borno.


Wakilinmu ya ruwaito wani jami’in leƙen asiri yana shaida wa Zagazola Makama cewa, ISWAP ta yi wa mayaƙan na Boko Haram kwanton ɓauna ne a yunkurinsu na sace dabbobin mutanen yankin da ke Arewacin Borno.


Kazalika, Zagazola ya ce baya ga kashe mayaƙan Boko Haram takwas da ISWAP ta yi, ta kuma samu nasarar ƙwace makamansu da babura.


A bayan nan dai ana zargin cewa yunwa ta addabi sansanonin kungiyar Boko Haram a yankin Bama a sakamakon ƙarancin abinci.


Bayanai sun ce hakan ce ta sa mayaƙan ke kai hare-hare a ƙauyukan yankin da gonaki don samun kayan abinci, kudi, magunguna da sauransu.


Anjwo cewa a ranar 3 ga watan Yuli, an gano gawarwakin manoma uku a Gajeri, wani kauye mai tazara kadan da Karamar Hukumar Konduga ta Jihar Borno, bayan wani hari da wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai musu.

Leave a Reply