INEC ta sanya ranar 16 ga Agusta don zaɓen cike gurbi a mazabu 16
Daga Shafaatu Dauda Kano
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓukan cike gurbi a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025, domin cike guraben kujeru a majalisun tarayya da na jihohi a faɗin jihohi 12 a Najeriya.
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyu a Abuja ranar Alhamis 25 ga Yuni, 2025.
Zaɓukan cike gurbin za su gudana ne domin cike guraben kujeru a Majalisar Tarayya da kuma Majalisun Dokoki na Jihohi, sakamakon murabus, rasuwa ko kuma soke zaɓe da kotu ta yi.
“Zaɓukan za su gudana a mazabu 16, ciki har da gundumomi biyu na Sanata, gundumomi biyar na majalisar wakilai, da kuma kujeru tara na majalisun jihohi,” in ji Yakubu.
KU KUMA KARANTA:Kotu tayi watsi da hukuncin zaɓen ƙananun hukumomin jihar Kano
Mazabun da za a gudanar da zaɓe sun haɗa da:
Sanatoci: Anambra ta Kudu da Edo ta Tsakiya
Majalisar Wakilai: Ovia South West/Ovia South East (Edo), Babura/Garki (Jigawa), Chikun/Kajuru (Kaduna), Ikenne/Shagamu/Remo North (Ogun), da Ibadan North (Oyo)
Majalisun Jihohi: Ganye (Adamawa), Onitsha North I (Anambra), Dekina/Okura (Kogi), Zaria Kewaye da Basawa (Kaduna), Bagwai/Shanono (Kano), Mariga (Niger), Karim Lamido I (Taraba), da Kauran Namoda South (Zamfara)