Ina jin daɗin Halin da jam’iyyun Adawa suke ciki – Shugaba Tinubu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa yana jin daɗin ganin jam’iyyun adawa na cikin rikici da rashin daidaito.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a zauren majalisar dokoki da ke Abuja a yau Alhamis, yayin bikin tunawa da ranar dimokuraɗiyya a Najeriya.
KU KUMA KARANTA: June 12: Tinubu zai yi wa ƴan ƙasa jawabi gobe
A cewarsa: “Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa a tagayyare. Ba zan ce ina fatan kun gyaru ba, ina ma jin daɗin ganin ku a haka.”
Wannan jawabi na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulki ke ci gaba da karɓar ɗaruruwan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa masu sauya sheƙa zuwa gareta.
Tinubu ya ce jam’iyyarsu ba za ta toshe ko hana kowa shiga cikinta ba, domin hakan na nufin tauye ‘yancin ɗan ƙasa.