IMC Kaduna, Ta Buƙaci Yan Jaridu Su Gudanar Da Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya

0
589

…Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Deborah Da Fatima

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR sasanci tsakanin mabiya addinai mabanbanta na Kaduna (IMC) tare da hadin gwiwar Community Peace Action Network (CPAN), sun bayyana kisan da wasu yan daba suka yiwa Deborah Samuel da Fatima (Harira) a matsayin dabbanci, rashin mutuntaka wanda ya zama abin Allah wadai a cikin duk wani addini na gaskiya.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan shirin (CIPP), Rabaran Dokta James Novel Wuye, a yayin taron wata-wata da kafafen yada labarai kan zaman lafiya, wanda kungiyar (IMC) Kaduna ta shirya kan shirin Community Initiatives to Promote Peace (CIPP) da aka gudanar a ranar Alhamis, mahalarta taron sun bayyana cewa, matsalar masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami da rikicin manoma da makiyaya a wasu sassan kasar nan, musamman na watan Mayun 2022 na da matukar tayar da hankali.

Bugu da ƙari, mahalarta taron sun kara da cewa yawan laifukan da ake aikatawa a yanzu na sanya rayuwar al’umma cikin haɗari, duba da yin la’akari da raguwar ƙoƙarin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen samar da tsaro na daga cikin abubuwan da ke kara haifar da su.

Sun yi Allah-wadai da kisan Deborah Samuel da wasu abokan karatunta suka yi a Sokoto da kuma kisan wata mata mai juna biyu daga Arewa da ‘ya’yanta hudu da yan kungiyar IPOB suka yi tare da yaba wa al’umma masu sa ido kan zaman lafiya, kafafen yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki kan yadda suka dakile wannan tashin hankali ta hanyar rahotanin da suka bayar a Kafafen sadarwa.

Mahalarta taron sun koka kan yadda ake samun karuwar kungiyoyin asiri a wasu sassan kasar nan, sun kuma bukaci hukumomi da su yi abin da ya kamata, musamman don hana matasa shiga irin wadannan kungiyoyi.

Sun bukaci dukkan shugabannin addini da cibiyoyin mafi rinjayen al’umma da su amince tare da girmama addinin sauran mutane, na Kiristanci da Musulunci kana su nisanci yin wa’azin tsokana ga mabiyansu musamman a Coci da Masallatai.

Mahalarta taron sun yabawa kafafen yada labarai da masu sa ido kan zaman lafiya a jihar Kano bisa rawar da suka taka a kan lokaci wajen ganin an dakile rikicin abun da ya fashe ta hanyar sanar da cewa tukunyar iskar gas ne ta fashe a yankin Sabon Gari na jihar, inda suka ce kokarin nasu ya taimaka wajen dakile tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar nan.

Hakazalika, sun yabawa kafafen yada labarai kan fallasa kungiyar ta’addanci kan daukar wasu mutanen kauyuka a jihar Kaduna.

Sun lura da yadda ‘yan daba na siyasa ke karuwa gabanin zabukan 2023, sun kuma yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su binciki ayyukansu ta yadda za a samu yanayi da zai ba da damar gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci a cikin kasar nan.

IMC, ta yi kira ga kafafen yada labarai da su bi ka’idojin da’a na wannan sana’a a cikin rahoton na su kuma su guji tunzura jama’a ta yadda za su haifar da tashin hankali da karya doka da oda.

A karshe mahalarta taron sun koka kan mallakar kananan makamai a tsakanin wasu mutane bisa zargin dogaro da kansu da ‘yan ta’adda, suna masu nuni da cewa hakan na iya kawo wa kasar rikicin kabilanci ko addini.

Leave a Reply