IG ya baiwa DPO Kano lambar yabo, bisa ƙin amincewa da karɓar cin hancin $200,000

0
468

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya bayar da takardar shaidar karramawa ga jami’in ‘yan sanda mai aiki a yankin Nasarawa a jihar Kano, SP Daniel Itse Amah, bisa ƙin amincewa da dala 200,000 da aka ba shi a matsayin cin hanci, a wani lamari na fashi da makami.

A cikin wata wasikar yabo, SP Amah ya samu yabo bisa yadda ya nuna ƙwarewa da jajircewa wanda ya kai ga kama Ali Zaki, lauyan da ke Kano da wasu jami’an ‘yan sanda.

An tattaro cewa binciken da jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin SP Amah suka yi ya kai ga cafke ‘yan fashi da makami a Kano.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an mayar da shari’ar zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja bisa umarnin IGP domin gudanar da bincike mai zurfi.

Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya tabbatar da kamen, inda ya ƙara da cewa “lauyan da sauran waɗanda ake zargi da hannu a cikin lamarin na da ƙarar da za su amsa kuma har yanzu muna kan lamarin”.

Leave a Reply