Hukumar tace fina-finai a Kano ta dakatar da nuna fina-finai 22, ciki har da Labarina da Daɗin Kowa
Daga Ibraheem El-Tafseer
Hukumar tace Fina-finai ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Alh. Abba El-Mustapha, ta dakatar da nuna fina-finai 22 da suka hada da Labarina, Gidan Sarauta, Ɗakin Amarya da Daɗin Kowa, bisa laifin kin gabatar da su don tantancewa kafin sakin su a kafafen yaɗa labarai.
Hukumar ta ce wannan mataki na da nufin tsaftace masana’antar Kannywood da kare al’umma daga fina-finai marasa inganci.
KU KUMA KARANTA: Na samu goyon bayan da nake buƙata a Kannywood – Daraktan Fim Ɗin Mai Martaba
Hukumar ta ba wa nasu fina-finai wa’adin mako guda daga 18 zuwa 25 ga Mayu, 2025, don gabatar da fina-finan da aka dakatar domin tantancewa.
Hukumar ta bukaci hadin gwiwar gidajen talabijin da hukumar NBC wajen tabbatar da bin doka.
Ga cikakken jerin sunayen fina-finai da aka dakatar kamar haka:
1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wa yasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Dadin Kowa
20. Tabarma
21. Kishiyata
22. Rigar Aro