Hukumar JAMB ta roƙi ‘yan majalisa kan cin gashin kansu, a cire su daga kasafin kuɗin ƙasa

2
819

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta buƙaci majalisar wakilai ta baiwa hukumar jarabawar cin gashin kanta ta fannin kudi.

Magatakardar hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede wanda ya yi wannan roƙo a madadin hukumar jarabawar ya bukaci ‘yan majalisar da su cire su daga cikin kasafin kuɗin ƙasa na shekara.

Ya yi wannan kiran ne a ranar Larabar da ta gabata lokacin da ya bayyana hakan a gaban kwamitin majalisar wakilai kan tsarin kashe kudade na matsakaicin wa’adi (MTEF). Ya ƙara da cewa a shekarar 2017, bayan fitar da Naira biliyan 7.5, hukumar jarrabawar ta sake duba kuɗaɗen rajistar ta daga N5,000 zuwa N3,500.

Sai dai Oloyede ya ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta bar hukumar ta JAMB ta koma farashin baya, duba da yadda tattalin arziƙin ƙasar nan ke ci gaba tashi.

Ya ce, “Babu inda gwamnati ke karɓar ƙananan kuɗi a wannan nau’in jarabawar. Gwamnati takan ba da wasu tallafi ga cibiyar saboda ɗalibai suna biyan kudi ƙalilan a matsayin kuɗin rajista, kuma daga gare ta, suna ɗaukar nauyin albashi kuma suna ba da wasu tallafi.

“Mun yarda a cire mu daga kasafin kudin, amma akwai sharudda. Ɗaya daga cikin sharuddan misali, lokacin da ɗalibai suka yi rajista a shekarar 2016, mun karɓi Naira 5,000, kuma hakan ya shafe shekaru biyar kafin na shiga. “A lokacin da muka shigo, mun tara Naira biliyan 7.5. Sai mulaga abin ya yi yawa, sai muka tuntuɓi gwamnatin tarayya domin ta rage kuɗaɗen. Tun daga nan ba mu ƙara Kobo ba.

“Na yi imanin ya kamata mu koma kan N5000 da muke karɓa. Idan aka yi la’akari da hauhawar farashin kayayyaki, Alal misali idan muka karbi Naira 10,000 – babu wanda zai nemi gwamnatin tarayya kobo ɗaya. “Babu wata ƙasa ko’ina a duniya, (sai dai wata ƙila ƙasar Finland)- wanda suke karbbar kuɗi kaɗan kamar yadda JAMB ke karba. A Finland, mun san cewa komai kyauta ne, ”in ji shi.

2 COMMENTS

Leave a Reply