Hukumar Hizba a Kano, ta haramta sauraron waƙar ‘Amanata’ ta Hamisu Breaker

0
94
Hukumar Hizba a Kano, ta haramta sauraron waƙar 'Amanata' ta Hamisu Breaker

Hukumar Hizba a Kano, ta haramta sauraron waƙar ‘Amanata’ ta Hamisu Breaker

Daga Shafaatu Dauda Kano

Rundunar Hisbah ta Jihar Kano ta nuna ɓacin ran ta, da bakin ciki akan wata waƙa da mawaƙi Hamisu Breaker, ya rera mai suna Amana ta, inda rundunar tace akwai kalaman batsa a cikin ta.

Mataimakiyar babban kwamandan rundunar a bangaren Mata Dr. Khadija Sagir, ce tayi ala wadai da wakar, sannan ta nemi matasa su dena sauraron wakar.

KU KUMA KARANTA:Hisbah a Kano ta rushe wurin da ake cewa sawun Annabi (SAW) ne ya fito

Hisbah tace wakar na dauke da abubuwan da ke goyon bayan aikata alfasha, musamman yadda mata ke rawa da kuma amfani da kalmomin batsa a cikin bidiyon wakar.

Dr. Khadija ta kara da cewa bisa abinda ke cikin wakar, an dauke ta a matsayin haramun a karkashin koyarwar addinin Musulunci.

Leave a Reply