Hukumar Hizba a Kano ta gargaɗi masu cewa, wata mata ta mutu ta dawo

0
83
Hukumar Hizba a Kano ta gargaɗi masu cewa, wata mata ta mutu ta dawo

Hukumar Hizba a Kano ta gargaɗi masu cewa, wata mata ta mutu ta dawo

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi gargadi ga al’umar karamar hukumar Kura a jihar Kano da su guji yada jita-jita, akan al’amari wata mata Aisha Uwa Ibrahim, mai rangwamen hankali da ake cewar wai ta mutu kuma ta dawo.

Ita dai Aisha, ta bace ne kuma ana tsakiya da neman ta sai kuma wata mata daban da ake ganin sun yi kama ta gamu da hadari mota ta buge ta a bakin titi, ta samu munanan raunuka a fuskarta ta yadda ba za,a iya gane ta ba.

Nan da nan mutane ba tare da zurfin bincike ba, su ka ce Aisha ce da ake nema.

Ba tare da bata lokaci ba aka kai ta gida, aka yi mata sutura da zaman makoki dama karbar gaisuwa,

Daga baya ne kuma, ita Aisha da ake nema aka ganta a garin Kibiya, inda dawo da ita gida.

Bayan ta dawo ne kuma, nan da nan iyaye da Yan uwa dama abokan arziki suka fara farinciki matuka, nan da nan labarin Aisha ya karade yankin karamar hukumar Kura.

KU KUMA KARANTA:Hukumar Hisbah a Kano ta haramta wasan tashe a faɗin Jihar

A zantawarta da wakilin Neptune Prime, mahaifiyar Aisha, wato Habiba Ibrahim ta ce da ma ita ba ta ga gawar ta ba, in da ta ce, wadanda su ka yi mata wanka ne su ka sanar cewar sun shaida kafafunta da hannaye, amma ta samu rauni a fuska yadda ba za,a iya ganeta ta fuskarta ba.

Da ya ke zantawa da manema labarai, shugaban hukumar hisba na karamar hukumar Kura, Ustaz Ali Alkassim Kura
Ya yi kira ga mutane da su guji yada jita-jitar cewar Aisha ta mutu ta dawo.

“A koyarwar addinin musulunci, mutum ba ya mutuwa ya dawo, Duk mutumin da ya ke tunanin hakan zai iya yiwuwa to ya binciki imaninsa.

Musulmi su guji abinda zai iya taba musu imani, wannan kuskure ne, a gari kamar Kura, mai dimbin tarihi akan addini da alkur’ani a ce an samu irin wannan kalami ”

“Baiwar Allah wacce ta rasu an sameta, kuma a matsayinta na musulma, hakki ne na musulmi a yi mata sutura, kuma an yi mata sutura. Sannan, Karshe wacce ake tunanin ita ce ta rasu, ba ita ba ce, kuma Allah ya dawo da ita gida. Wacce ta rasu aka yi mata sutura, mu na yi mata mata addu’ar Allah Ya yi mata rahma. Ita kuma maras lafiya Aisha, mu na addu’ar Allah Ya bata lafiya.” A cewar Ustaz Ali Alkassim Kura.

Leave a Reply