Hawan Sallah: Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe

0
134
Hawan Sallah: Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe

Hawan Sallah: Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe

Daga Ibraheem El-Tafseer

Majalisar Masarautar Bauchi ta janye soke hawan Daushe da ta yi da fari, inda ta ce a yanzu za a gudanar da hawan Sallah ƙarama kamar yadda aka saba duk shekara.

Idan za a tuna dai da farko masarautar ta nemi ɗage Hawan Daushe na bana inda gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya amince da hakan. Sai dai, ‘yan awannin da fitar sanarwar, masarautar ta janye haramcin inda ta tabbatar wa jama’a cewa za a yi hawan Daushe.

A wata sanarwar da Magatakardan Majalisar Alh. Shehu Mudi Muhammad ya fitar a ranar Asabar ya ce bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki kan lamarin ne aka amince za a yi hawan.

“Majalisar Masarautar Bauchi tana farin cikin sanar da jama’a cewa yanzu za a gudanar da bukukuwan Hawan Sallah na shekarar 2025 kamar yadda aka tsara.

“Bayan nazari da tuntuɓar gwamnatin jihar Bauchi, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya amince da ci gaba da gudanar da wannan gagarumin biki.”

“Bikin Sallah wani muhimmin ɓangare ne na al’adunmu, kuma muna farin ciki tare da marhabin da mazauna, maziyarta, da masu yawon buɗe ido don halartar bukukuwan sallan bana.”

Sanarwar ta ce za a sanar da cikakken bayanai game da jadawali da shirye-shiryen hawan nan ba da jimawa ba, “Muna addu’an Allah ya karbi ibadunmu kuma yasa ayi hidiman cikin nasara,” sanarwar ta ƙara shaidawa.

KU KUMA KARANTA:Masarauta: Ba mu da fargaba kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara – Gwamnatin Kano

Tun da farko dai a cikin sanarwar manema labarai da kakakin gwamnan jihar Bauchi Mukhtar Gidado, ya sanar da cewa Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da matsayar da kwamitin masarautar Bauchi kan hawan Sallah ya ɗauka na ɗage bikin hawan Sallah da ke kira da hawan Daushe na bana.

Bisa al’ada dai an saba gudanar da hawan Daushe inda masu riƙe da sarautu da sarakuna ke hawan dawakai da shiga ta alfarma tare da baje kolin nau’ikan al’adun gargajiya lamarin da ke zama abun sha’awa musamman ga masu yawan buɗe ido.

Kazalika, hawan ya zama wani dandali na haɗa kan al’umma da bunƙasa al’adun gargajiya. Sannan, an saba yin amfani da hawan wajen gudanar da shagulan bikin sallah a kowace shekara.

Daga bisani kuma Masarautar Bauchi ta ce, wasu na neman juya haƙiƙanin labarin da aka bayar na cewa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya amince da buƙatar neman izinin ɗage hawan Daushe na bana.

Masarautar ta ce, kwamitin kula da hawan Sallah ne ya soke hawan tare da neman amincewa daga wajen gwamnatin jihar.

Sai dai bayan dukkan wannan, yanzu masarautar ta tabbatar da cewa za a yi hawan kamar yadda aka saba duk shekara.

Leave a Reply