Harin ƙunar baƙin wake ya kashe mutane 6 a Borno – ‘Yansanda

0
108
Harin ƙunar baƙin wake ya kashe mutane 6 a Borno – ‘Yansanda

Harin ƙunar baƙin wake ya kashe mutane 6 a Borno – ‘Yansanda

Daga Ibraheem El-Tafseer

Aƙalla mutane shida ne suka mutu inda wasu 15 suka jikkata a wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai a garin Gwoza na jihar Borno.

Wani abin takaici ya faru ne a lokacin da ‘yar ƙunar baƙin wake ta tayar da bam a garin Gwoza, ranar Asabar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, (NAN), ya ruwaito cewa an kai harin ne a wani wurin shaƙatawa na motoci da ake ƙira Marrarraban Gwoza.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Borno Yusuf Lawal ya tabbatar da faruwar harin yana mai cewa wata ‘yar ƙunar baƙin wake ce ta kai harin.

Lawal ya ce jami’in ‘yansandan shiyyar Gwoza ne ya sanar da shi cewa aƙalla mutane shida ne suka mutu inda aka kwashe wasu 15 zuwa asibiti.

Wani ganau mai suna Buba, ya shaida wa NAN cewa ‘yar ƙunar baƙin waken ta nufi tsakiyar wani bikin aure ne, inda ta tayar da bam ɗin a nan.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

Buba ya ce harin ya rusa farin ciki da murnar wannan rana ta musamman, inda ya bar iyalai da ‘yan uwa cikin makoki.

Wani wanda ya shaida lamarin, Muhammed Kasim, ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana.

“Mun ji ƙarar fashewar abubuwa, tare da ƙura, sai muka ga gawarwaki a ƙasa.”

Ya ce an kwashe da dama daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti yayin da aka tura jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya a yankin. (NAN).

Leave a Reply