Hajjin bana: Saudiyya ta hana ɗaukar hoto da taron siyasa a guraren ibada
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumomin Saudiyya sun hana daukar hoto, taruka da al’amuran siyasa da daga tutoci a wuraren ibada yayin aikin Hajjin bana na 2025.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fitar, masarautar ta bayyana cewa mahajjata ba su da izinin daukar hoto ko yin bidiyo a Masallacin Harami da ke Makkah, da Masallacin Annabi da ke Madinah, da kuma muhimman wuraren aikin hajji irin su Mina, Arafat da Muzdalifah.
KU KUMA KARANTA:Za a fassara Huɗubar Hajjin bana zuwa harsuna 34 a ranar Arfa
Ma’aikatar ta ce wannann umarni ya shafi wayoyin hannu da kuma na’urorin daukar hoto na kwararru, tare da gargadin kada a daga tuta ko alluna da ke dauke da alamomin siyasa, kabila ko akida.
Hukumomin sun sake jaddada cewa irin wadannan ayyuka na iya lalata yanayin ibada da kuma haifar da rarrabuwar kai tsakanin mahajjata.