Gwamnatin tarayya za ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan daidaita farashin man fetur

0
94
Gwamnatin tarayya za ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan daidaita farashin man fetur

Gwamnatin tarayya za ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan daidaita farashin man fetur

Daga Jameel Lawan Yakasai 

Gwamnatin tarayya ta tsara ranar 23 da 24 ga watan Yuli domin gudanar da taron kasa na masu ruwa da tsaki don tattauna batutuwan da suka shafi farashin man fetur da kuma ƙalubalen samar da shi a sashen kasuwancin man fetur, a yayin da ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu ke kara kira ga kafa dokokin daidaita farashi.

Francis Ogaree, Darakta-Janar na fannin Sarrafa Man Fetur, Shigarwa da Hanyoyin Sufuri a Hukumar NMDPRA, ne ya sanar da wannan taro yayin wani zama na musamman a makon makamashi na Najeriya karo na 24 da aka gudanar a Abuja.

KU KUMA KARANTA: Kanfanin man NNPC ya rage farashin litar man fetur a Kano da Jigawa

Ya ce NMDPRA za ta shirya wannan taro, wanda zai haɗa ‘yan kasuwa, masu tace mai, masu aiki da masana’antu da jami’an gwamnati don tattauna kan yadda za a kafa tsarin farashi, samar da kayan aiki (feedstock), da hanyoyin da za a daidaita kasuwar man fetur da aka sake warewa daga tallafin gwamnati.

Ogaree ya bayyana bukatar yin tattaunawa domin karfafa tsarin farashin man fetur a wannan zamani na bayan cire tallafi.

A yayin jawabi a zaman, Ogaree ya ce hukumar tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki “a wajen taronmu, inda muke magance matsaloli da kuma samar da mafita.”

Leave a Reply