Gwamnatin tarayya ta soke faretin bukin ranar Dimokuraɗiyya

0
60
Gwamnatin tarayya ta soke faretin bukin ranar Dimokuraɗiyya

Gwamnatin tarayya ta soke faretin bukin ranar Dimokuraɗiyya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnatin Tarayya ta soke faretin sojoji da ake yi don tunawa da Ranar Dimokuraɗiyya ta shekara-shekara, wadda za a gudanar da bikin ta a ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni a matsayin cika shekara 26 da dimokuraɗiyya ta dawo Najeriya.

Bayanan da Kwamitin Harkokin Bikin Ranar Dimokuraɗiyya na Ma’aikatu da dama ya fitar sun nuna cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar ƙasa baki ɗaya da misalin ƙarfe 7 na safe ranar Alhamis, ba tare da an gudanar da faretin Ranar Dimokuraɗiyya kamar yadda aka saba a baya ba.

KU KUMA KARANTA: June 12: Tinubu zai yi wa ƴan ƙasa jawabi gobe

Maimaikon faretin, Shugaba Tinubu zai halarci zaman haɗin gwiwa na musamman da za a gudanar a Majalisar Tarayya da ƙarfe 12 na rana.

Ana sa ran wannan zaman haɗin gwiwa zai ƙunshi jawaban da suka shafi halin da ƙasa ke ciki, tunawa da tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya, da kuma kiran da ake sabunta wa na haɗin kan ƙasa da sauye-sauyen da suka daɗe ana buƙata.

Leave a Reply