Gwamnatin tarayya haɗe da ISDB, AFDB za su tallafawa manoma ƙarƙashin shirin SAPZ a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Gwamnatin Taraiya, tare da haɗin gwiwar bankin Musulunci, ISDB da Bankin Afirka AFDB da gwamnatin Kano za su tallafawa manoma a jihar.
An samar da shirin ne domin karfafawa da bunƙasa tattalin arzikin manoman shinkafa, ridi, tumatur da gyada a jihohi bakwai da su ka hada da Kano, Imo, Kaduna, Cross River, Kwara, Oyo, Ogun da Abuja.
Da ya ke jawabi a yayin taron wayar da kai a kan shirin ga manoma a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Kumbotso, shugaban shirin a Kano, Aminu Abdullahi Iliyasu, ya ce kananan hukumomi 16 ne za su amfani da shirin a jihar.
KU KUMA KARANTA:Hukumar tace fina-finai a Kano ta rufe ta kama wasu ‘yan wasa
A cewar sa kananan hukumomin sun hada da Dawakin Kudu, Kumbotso, Tofa, Gwarzo, Madobi, Shanono, Minjibir, Gabasawa, Bebeji Dambatta, Gezawa, Garun Malam, Shanono, Minjibir, Makoda da Kura.
Ya kara da cewa an yi taron ne don ilmantar da manoma, masu sayar da kayan abinci da yan kasuwa da kuma masu ruwa da tsaki kan amfanin shirin.
Ya ce taron wayar da kan an hada shi ne da nufin ilmantar da manoman shinkafa da tumatur da ridi da gyada, musamman mata da matasa domin bunkasa tattalin arzikin al’umma.
Su ma manoman da su ka halarci taron sun nuna jin dadi da gamsuwa game da bayanan da suka samu akan shirin na SAPZ, inda su ka nuna aniyar su ta yin duk me yiwuwa wajen ganin shirin ya samu nasara a Kano.