Gwamnatin Neja ta hana yin bukukuwan babbar Sallah a jihar
Daga Shafaatu Dauda Kano
Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya bada umarnin rage shagulgulan bikin Sallah da dakatar da Hawan Bariki da sauran manyan tarukan Sallah a dukkan masarautun jihar.
Wannan umarni ya biyo bayan mummunar ambaliya da ta auku a Mokwa da kewaye, wacce ta yi sanadin salwantar rayuka da dukiyoyi.
KU KUMA KARANTA: Kifewar jirgin ruwa ta kashe mutane da dama a jihar Sokoto
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abubakar Usman, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce an yanke wannan shawara a matsayin girmamawa ga wadanda lamarin ya rutsa da su, da kuma ba da damar yin addu’a ga waɗanda suka gamu da iftila’in.
Yayin da yake isar da umarnin Gwamnan ga masarautu, Sakataren Gwamnatin ya ce ambaliyar Mokwa na daya daga cikin abu mafi muni da aka taba fuskanta a jihar cikin shekaru masu yawa da suka shuɗe inda ta bar wasu ba gida, wasu kuma suka rasa ‘yan uwansu da dukiyoyinsu.