Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 8.5 don aikin magance zaizayar ƙasa a unguwanni 2 a jihar

0
40
Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 8.5 don aikin magance zaizayar ƙasa a unguwanni 2 a jihar

Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 8.5 don aikin magance zaizayar ƙasa a unguwanni 2 a jihar

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da kwangilar da ta kai naira ₦8,497,595,290.00 domin aikin magance ambaliyar kwazazzabai da zaizayar kasa a unguwannin Bulbula da Gayawa a kananan hukumomin Ungogo da Nassarawa na jihar.

Wadannan unguwanni biyu sun daɗe suna fuskantar matsananciyar zaizayar ƙasa, wacce ta haifar musu da asarori na rayuka da dukiyoyi, ba tare da gwammnati ta kai musu ɗauki ba.

Da ya ke jawabi bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar a Kano a yau Laraba, kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahir M. Hashim, ya bayyana cewa an ba da aikin ne ga kamfanin Habib Engineering kan kudin ₦8,497,595,290.00, kuma za a kammala shi cikin kwanaki 715.

KU KUMA KARANTA:Tinubu ya rattaɓa hannu kan kasafin kuɗin 2025

Hashim, wanda kuma shi ne Shugaban shirin ACRESAL, ya ce wannan aikin babban mataki ne wajen kare rayuka da hanyoyin samun abinci na al’ummar Bulbula da Gayawa, waɗanda ambaliyar kwazazzabai ta addaba na tsawon shekaru.

Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kawo ɗauki ga waɗannan yankuna da su ka kwashe sama da shekaru 20 a halin ƙaƙanikayi sakamakon zaizayar ƙasa.

Ya tabbatar da cewa za a kammala aikin akan lokaci kuma al’ummar yankuna za su samu ci gaban tattalin arziki sakamakon bunƙasar sana’o’in su da za a samu bayan aikin.

Leave a Reply