Gwamnatin Kano ta tabbatar da tattara Miliyan 15 ga ƙananan hukumomi 44 domin sayawa Sarkin Kano mota

0
106

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin Kano ta tabbatar da tattara miliyan sha biyar-biyar daga ƙananan hukumomi 44 na jihar domin sayawa masarauta motoci.

A tattaunawar Jaridar Neptune Prime da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano Comr Ibrahim Waiya, ya tabbatar batun sayen motocin, inda ya ce ba sabon abu bane.

KU KUMA KARANTA:Masu ƙwacen waya a Kano sun kashe ɗalibin Jami’ar Bayero

Wasu rahotanni ne dai suka tabbatar da za’a sayawa masarautar motoci da suka hada da Toyota Land Cruiser VXR 2024 kan Naira miliyan 268, da Toyota Hilux 2024 kan Naira miliyan 98, da motar Toyota bas kan Naira miliyan 98, da kuma mota kirar Prado 2024 kan Naira miliyan 156, Kwamishina Waiya ya kara da cewar zakoma a gyara waɗanda suka lalace.

Leave a Reply