Gwamnatin Kano ta naɗa Ahmed Musa a matsayin manajan Darakta na Kano Pillars

0
99
Gwamnatin Kano ta naɗa Ahmed Musa a matsayin manajan Darakta na Kano Pillars
Kyaftin ɗin Najeriya, Ahmed Musa

Gwamnatin Kano ta naɗa Ahmed Musa a matsayin manajan Darakta na Kano Pillars

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa kaptin ɗin tawagar Super Eagles, Ahmed Musa a matsayin babban shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.

KU KUMA KARANTA: Usman Abdallah ya ajiye aiƙin Horars da Ƙungiyar Kwallon ƙafa ta Kano Pillars

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce naɗin wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa ƙungiyar kafin fara sabuwar kakar Premier ta Najeriya.

Kuna ganin wannan naɗi zaiyi tasiri a ƙungiyar wajan farfaɗo da tasirin sai masu gida?

Leave a Reply