Gwamnatin Kano ta karyata zargin ciwo bashin Dala Miliyan 6.6 da wasu ƴan APC suka yi mata

0
75
Gwamnatin Kano ta karyata zargin ciwo bashin Dala Miliyan 6.6 da wasu ƴan APC suka yi mata

Gwamnatin Kano ta karyata zargin ciwo bashin Dala Miliyan 6.6 da wasu ƴan APC suka yi mata

Daga Jameel Lawan Yakasai

Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin da wata ƙungiyar magoya bayan jam’iyyar APC ta yi, cewa gwamnatin NNPP ta ciyo sabon bashi na dala miliyan 6.6 tun bayan hawanta mulki a shekarar 2023.

Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban hukumar kula da basuka ta jihar Kano, Dr. Hamisu Sadi Ali, ya fitar.

Ya ce tun daga lokacin da gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf ta hau mulki, ba ta rattaba hannu ko ciyo wani sabon bashi na cikin gida ko na waje ba, sai dai ma tana ci gaba da biyan bashin da tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta bari a shekarunta takwas na mulki.

KU KUMA KARANTA: Rundunar Ƴansanda ta Kano ta gano AK-47 ta bogi a gidan daya daga cikin wadanda ake zargi da kisan DPO na Rano

Sanarwar ta caccaki jagoran ƙungiyar, kuma tsohon Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji, inda ta ce siyasa ta rufe masa ido wajen fahimtar dokar da aka kafa hukumar kula da basussuka da ita a 2021.

Dr. Hamisu ya ce idan har ƙungiyar ta APC Patriotic Volunteers ta ziyarci hukumar kula da basussukan tarayya (DMO) a Abuja kamar yadda ta ce, to ya kamata ta fito da cikakkun hujjoji da suka haɗar da sunan wanda aka karɓo bashin daga wajensa, yarjejeniyar bashi, dalilin bashin, tsarin biyan bashin, nau’in bashin ko, da sauran takardu da za su tabbatar da cewar da gaske an ciyo bashin.

Ya ƙara da cewa, “mutane yanzu sun waye sosai, ba za ka fito da zargi mara tushe ka yi tsammanin za a ɗauke ka da zarginka da muhimmanci ba.”

Leave a Reply