Gwamnatin Kano ta ba da umarnin farfaɗo da makarantar Faransanci da Sinanci a jihar
Daga Shafaatu Dauda Kano
A ƙoƙarinsa na bunƙasa ɓangaren ilimi da inganta koyo da koyarwa a jihar Kano, Gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya ba da umarnin a gaggauta gyara makarantar koyon harsunan Faransanci da Sinanci mallakar gwamnatin jihar.
Umarnin gwamnan ya biyo bayan wata ziyarar bazata da ya kai makarantar da ke garin Kwankwaso, a ƙaramar hukumar Madobi, kamar yadda sanarwar da Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya aiko wa Manema labarai ta bayyana.
KU KUMA KARANTA: Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta gano wasu bama-bamai 9 da basu fashe ba
A cewar Gwamnan, “Na kai ziyara makarantar ne domin na ganewa idona yadda ɗalibai da malamai ke gudanar da harkokinsu, da kuma yanayin gine-ginen makarantar”.
Gwamnan ya bayyana jin daɗinsa bisa ƙwazon malamai da ɗaliban, musamman yadda ɗaliban ke iya magana da kyau da harsunan Faransanci da Sinanci.
“Za mu gyara makarantar ba tare da ɓata lokaci ba, adan haka na umarci Kwamishinan aiyuka da ya hanzarta fara aikin gyaran gine-ginen da suka lalace a makarantar”.
A ƙarshe sanarwar ta ce wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin Kano, na inganta ilimi da samar da ingantacciyar nagarta a fannin koyon harsuna domin bunƙasa ci gaban jihar.