Gwamnatin Kano ta ƙona gurɓatattun miyagun ƙwayoyin jabu

0
99
Gwamnatin Kano ta ƙona gurɓatattun miyagun ƙwayoyin jabu

Gwamnatin Kano ta ƙona gurɓatattun miyagun ƙwayoyin jabu

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Gwamnatin Kano ta ƙona gurɓatattun miyagun ƙwayoyin jabu da kuma waɗanda lokacin aikin su ya ƙare (expired), wanda kwamitin yaƙi da miyagun Ƙwayoyi da kwacen waya na jihar karkashin jagorancin birgediya janal Gambo yar aduwa mai ritaya su ka kama. Da kudin su ya kai naira biliyan biyu da rabi.

KU KUMA KARANTA:Al’ummar Gwammaja a Kano sun shiga jimamin tunawa da rashin da sukai na faɗuwar Jirgin sama a yankin

Gwamnan Kanon Alh. Abba Kabir Yusuf ta bakin kwamishinan ma’aikatar kimiyya da fasaha kuma shugaban kwamitin Samar da zaman lafiya na jihar Dr. Yusuf Ibrahim kofar mata, ya ce gwamnatin na dauki matakin dakile amfani da miyagun kwayoyin ne sakamakon yadda ta ke kaunar al’ummar ta.

Kasancewar idan aka bar al’umma suka yi amfani da magungunan da wa’adin aikinsu ya kare za su sami matsala alafiyarsu.

Leave a Reply