Gwamna Zulum ya sake buɗe kasuwar shanu ta Gamboru

2
679

Gwamnan jihar Borno Baba Gana Umara Zullum ya sake buɗe kasuwar shanu ta Gamboru da ke jihar bayan ta shafe shekara bakwai tana rufe bisa dalilin rikicin Boko Haram.

Babagana Umara Zulum, ya yaba wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da rundunonin tsaron Najeriya waɗanda ya ce da taimakonsu ne zaman lafiya ya samu kuma hakan ne dalilin sake buɗe kasuwar.

Kasuwar Shanu ta Gamboru ita ce babbar kasuwar dabobbi da ta haɗa ƙasashen Najeriya da Kamaru da Chadi, wace ke samar da shanu a yankin Arewa maso gabas da sauran sassan ƙasar.

2 COMMENTS

Leave a Reply