Gwamna Buni ya nemi haɗin kan jami’o’in Burtaniya uku, don bunƙasa harkar ilimi a jihar Yobe

0
291

Daga Ibraheem El-Tafseer

Alhaji Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe, ya isa ƙasar Ingila domin yin bincike da kuma amfani da ɓangarorin haɗin gwiwa don inganta harkar ilimi a jihar.

Gwamna Buni zai yi tattaunawa mai mahimmanci tare da shahararrun Jami’o’i uku da suka haɗa da Jami’ar Sussex, Jami’ar York da Cibiyar Crick.

Ana sa ran ziyarar za ta jawo tallafin ilimi ga cibiyoyi a jihar.

Idan dai za a iya tunawa a baya wasu daga cikin cibiyoyin sun tallafa wa jami’ar jihar Yobe da kayan aiki tare da yin alƙawarin kafa cibiyar bincike a jami’ar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya amince da ɗaukar ma’aikatan jinya 158, da ba da alawus ga ɗalibai 393

Gwamnan zai kuma yi amfani da wannan ziyarar domin lalubo wasu ɓangarorin da za su taimaka wajen kawo sauyi a fannin ilimi ta hanyar gaggawar da aka ayyana a fannin.

Ko shakka babu ziyarar waɗannan cibiyoyi za ta sauƙaƙa yunƙurin gwamnatin jihar na inganta ilimi a jihar Yobe.

Leave a Reply