Gobara ta ƙone shaguna 47 a kasuwar waya ta a Kano

0
133
Gobara ta ƙone shaguna 47 a kasuwar waya ta a Kano

Gobara ta ƙone shaguna 47 a kasuwar waya ta a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

A jiya Juma’a ne dai ibtila’i ya faɗawa shahararriyar kasuwar waya ta Farm Centre a jihar Kano, yayin da gobara ta kama, har ta ƙone shaguna 47, lamarin da ya janyo asarar dukiya ta miliyoyin Naira.

A wata sanarwa da Kakakin Hukumar Kwana-kwana ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar, ya ce sun samu kiran kai-ɗauki da misalin ƙarfe 12:32 cewa gobara ta kama a kasuwar waya ta Farm Centre.

KU KUMA KARANTA: Mummunar gobara a Kano, ta ƙone shaguna 6 ƙurmus a kasuwar Kurmi

A cewar Abdullahi, tuni jami’an hukumar su ka garzaya wajen da lamarin ya faru kuma su ka sami nasarar kashe wutar.

Ya kara da cewa ginin da gobarar ta afku mai bene ne, inda wutar ta koma shaguna 20 da rumfuna 13 a ƙasa, sai kuma shaguna 13 da rumfa 1 da ke saman benen su ma su ka kone.

Sai dai kuma Kakakin ya baiyana cewa ba a samu asarar rai ko rauni ba, inda ya bayyana cewa fashewar batirin sola ce ta haifar da gobarar.

Leave a Reply