Gini ya ruguje, ya rufta kan mutane a hanyar Beirut Kano

1
237

Aƙalla mutane goma ne suka maƙale a wani bene mai hawa uku da ake ginawa a shahararriyar kasuwar titin Beirut da ke cikin birnin Kano.

Ba a tantance adadin mutanen da abin ya shafa ba, ciki har da wasu da ke aikin ginin. Wani ganau ya ce gwamnatin jihar Kano ce ta mallaki ginin. Ya tabbatar da cewa har yanzu mutane kusan goma suna maƙale a ginin da ya ruguje.

Ya zuwa yanzu dai, an ceto mutane uku, sai dai mazauna yankin na kokawa da rashin isar tawagar masu aikin ceton da wuri.

Wani ganau ya ce abokin sa na cikin waɗanda suka maƙale, yayin da aka kira lambar wayarsa, ya amsa, ya ce yana ta shaƙewa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 30:30 na yammacin Talata.

1 COMMENT

Leave a Reply