Gidauniyar Fasaudat ta tallafawa Fatima da aka yankewa ƙafa

0
483

Daga Saleh INUWA, Kano


Gidauniyar Fasaudat Support Foundation ta tallafawa yarinyar nan mai suna Fatima da ta rasa ƙafarta sanadiyar tuƙin ganganci da wani yaro yayi.

kUKUMA KARANTA: Matashi yayi sanadiyar yankewa budurwa ƙafa a Sokoto

Shugabar Gidauniyar, Hajiya Fatima Ahmad Maigari tareda sauran jagororin gidauniyar ne suka ziyarci Fatima a asibitin koyarwa ta jamiyar Danfodio wato UDUTH.

Hajiya Fatima Maigari ta nuna kaɗuwa da halin da Fatima ta sami kanta inda tace ta daukeshi a matsayin ƙaddara daga Allah.


Fatima Maigari ta bayarda tallafin kuɗi da wasu kayyaki ga fatima. An gudanar da adduoin samun lafiya ga Fatima.

Leave a Reply