Gasar kwallon Duniya: Qatar mai masaukin baƙi tasha kashi a hannun Ecuador

2
560

Ƙasar Qatar ta fara wasan gasar Kofin duniya da ƙafar hagu bayan da ta sha kashi a hannun Ecuador da ci biyu da nema a filin wasa na Al Bayt.

Enner Valencia ne ya zura duka ƙwallayen biyu kafin a je hutun rabin lokaci, bayan da na’urar taimaka wa alƙalin wasa ta VAR ta soke ƙwallon farko da ya ci.

‘Yan wasan Qatar sun shafe wata shida a sansani guda suna shirya wa gasar to amma duk da haka da alama haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.

A yayin da zakarun Afirka wato Senegal da kuma Netherlands wadda sau uku tana zuwa wasan ƙarshe a gasar ke cikin rukuni guda da Qatar ɗin, an yi tunanin wannan wasan shi ne zai iya zama mai sauƙi ga ƙasar ta Qatar.

2 COMMENTS

Leave a Reply