Ganduje ya Ajiye mukaminsa na Shugabancin Jam’iyar APC na Ƙasa

0
57
Ganduje ya Ajiye mukaminsa na Shugabancin Jam'iyar APC na Ƙasa

Ganduje ya Ajiye mukaminsa na Shugabancin Jam’iyar APC na Ƙasa

Daga Shafaatu Dauda Kano

A cikin wani mataki da ya ba da mamaki, Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, ya yi murabus daga mukaminsa nan take.

Ganduje, tsohon Gwamnan Jihar Kano, ya bayyana dalilin neman lafiya a matsayin abin da ya sa ya yanke shawarar saukadaga kujerar, yana mai cewa yana bukatar mayar da hankali kan lafiyarsa.

KU KUMA KARANTA:APC ta musanta cewa Ganduje ya sha da ƙyar a Gombe

Wata majiya ta rawaito cewa duk da cewa takardae murabus din na sa ta danganta saukarsa da batun lafiya, majiyoyi da ke da masaniya da al’amarin sun nuna cewa akwai yiwuwar rikici na siyasa a cikin jam’iyyar ya taka rawa wajen yanke shawarar da ya dauka.

Wata majiya ta rawaito cewa, ana danganta saukarsa da zarge-zargen almundahana da suka shafi harkar kuɗi, inda wasu mambobin jam’iyyar suka bayyana rashin jin daɗinsu kan “yawan bukatun kuɗi fiye da kima” da ofishinsa ke kakaba.

Leave a Reply