Galadiman Kano Abbas Sanusi, ya rasu yana da shekaru 92
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Allah Ya yiwa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi Bayero rasuwa cikin dare wayewar yau Laraba.
KU KUMA KARANTA:Ƙwararren ɗan jarida mai ɗaukar hoto, Zubairu Shaba ya rasu
Shi ne mahaifin shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas Sunusi, kuma guda daga cikin aminai, Yan gaba-gaba a wajen marigayi Sarkin Kano Ado Bayero.