Fusatattun matasa sun lakaɗawa kwamishina duka a wajen zaɓen fidda gwani

0
587

Banji Ajaka, kwamishinan lafiya na jihar Ondo, ya gamu da fushin matasa a jiya Asabar yayin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Daily Trust ta gano cewa Dakta Ajaka, wanda ke Mazaɓar Ugbo 3, a ƙaramar hukumar, ana zarginsa da ɓoye takardar sakamakon zaɓen.

Shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da suka yi da manema labarai, inda suka yi zargin cewa fusatattaun matasan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da ke adawa da tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne lokacin da ‘yan ɗaya ɓangaren na jam’iyyar suka buƙaci ganin takardar sakamakon zaɓen na fidda gwani.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

“Sun fusata ne suka buƙaci jami’in zaɓe ya ba su takardar sakamakon zaɓen sai kuwa ya ce ta na wajen Ajaka.

“Don haka suka yi masa duka a wurin, inda kuma garinsu ne. Jama’a sun fusata sosai da lamarin, inda rigimar ta ƙare a wajen.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Dakta Ajaka ya ce an zarge shi ne da riƙe takardar sakamakon zaɓen.

Ya yi bayanin cewa a lokacin da yake ƙoƙarin bayyana kansa, ’yan daban sun auka masa inda suka yi masa mugun duka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here