Fasinjoji (14) sun ƙone ƙurmus a wani mummunan haɗarin mota daya faru a jihar Kano

0
458

Wani hatsarin mota ya faru daga Gaya zuwa Wudil a mota ƙorar Toyota Hummer da wata mota ƙirar Hyundai jeep wanda hukumar kiyaye afkuwar hadura ta ƙasa FRSC ta tabbatar.

Motar bas mallakin Kano Line ta taho ne daga jihar Gombe a yayin da ta yi karo da motar ƙirar jeep, da misalin ƙarfe 7:30 na daren ranar Lahadi.

Kwamandan hukumar FRSC reshen jahar Kano, Zubairu Mato ya shaida wa manema labarai ranar Talatar nan cewa jami’an kiyaye haɗura sun isa wurin da haɗarin ya afku a ƙauyen Rege da ke Antukuwani, kan hanyar Kano zuwa Gaya da karfe 7:45 na yamma.

“Fasinjoji 13 ne suka kione ƙurmus nan take tare da jikkata wasu mutum 6 a haɗarin. An kuma sanar da rasuwar ƙarin mutum ɗaya daga cikin fasinjojin, macen da ta rasu a safiyar ranar Litinin a asibitin koyarwa na Aminu Kano, (AKTH) a sashin Intensive Care Unit.

Leave a Reply