Fargabar zaizayar ƙasa ta jefa al’ummar garin Harbau da ke Kano cikin ɗimuwa

0
78
Fargabar zaizayar ƙasa ta jefa al'ummar garin Harbau da ke Kano cikin ɗimuwa

Fargabar zaizayar ƙasa ta jefa al’ummar garin Harbau da ke Kano cikin ɗimuwa

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Yadda zaizayar ƙasa ta lalata hanyar shiga garin Harbau da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Mazauna garin sun shiga firgici a ya yin da zai zayar kasa ke cigaba da cinye garin, Malam Musa guda daga cikin mazaunin wannan kauye yace sakamakon zaizayewa da Kasar garin tafara ya sanya su cikin wani hali na rashin kwanciyar hankali a wannan yanki.

KU KUMA KARANTA:Annobar tsutsa ta mamaye gonakin Tumatir a Najeriya

“Zaizayar ƙasar na barazanar lalata maƙabartar yankin saboda yadda ruwan sama ke shiga ciki har ya rushe katangarta makabartar” a cewar sa.

“Shima wani maigidan shi mai suna Malam Shafi’i yace yanzu haka hankalinsu yafi tashi sakamakon karatowar damina, wanda a wannan lokaci ne yankin nasu ke kara afkawa cikin yanayin zai zayar kasar”

Daga karshe mazauna garin sunyi kira ga gwamna Abba Kabir Yusuf da ya kai musu ɗauki domin magance zaizayar ƙasar tare da samar musu da titin shiga garin.

Leave a Reply