Farfesa ya koma siyar da kayan miya saboda taɓarɓarewar tattalin arziki
Daga Shafaatu Dauda Kano
Nasir Hassan-Wagini, Farfesa a fannin albarkatun shuka a sashen ilimin halittu na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina, ya koma noma da sayar da kayan lambu don samun abin dogaro a wannan mawuyacin hali na taɓarɓarewar tattalin arziki da Najeriya ke ciki.
Farfesan yana yin wannan sana’a a kasuwar mako-mako da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, inda yake sayar da amfanin gonarsa.
Farfesa Hassan-Wagini ya shawarci matasan da suka kammala karatu su daina jiran samun aikin gwamnati, inda yace kamata yayi su fara ƙananan sana’o’i da noma don dogaro da kansu.
“Saƙona ga masu digiri, diploma da NCE shi ne su saki jiki su fara ƙananan sana’o’i a cikin unguwanninsu maimakon zaman banza,” in ji shi.
Ya bayyana cewa noma ya kasance cikin rayuwarsa tun yana yaro, inda ya gaji sana’ar daga mahaifinsa. Duk da cewa ya dade yana harkar noma da kasuwanci, amma sai bayan da ya zama farfesa mutane suka fara gane hakan.
KU KUMA KARANTA: An buɗe babbar kasuwar Singa a Kano bayan kammala aikin tsaftace magudanar ruwa
“Ni Farfesa ne a fannin albarkatun shuka a Jami’ar UMYU. Ina so matasa da ɗalibai su kalle ni, su ga matsayin da nake kai, amma har yanzu ina cikin ƙananan sana’a irin wannan,” in ji shi.
Farfesan ya soki halayen wasu matasa da ke kin shiga harkokin da za su amfanar da su, suna zaman jiran aikin da babu tabbacin samu.
Ya kuma gargadi matasa kan barin gida don yin hijira neman aiki, yana mai cewa ya kamata su mayar da hankali kan damammakin da ke kusa da su.
“Matasanmu su daina fita neman aiki a wasu wurare. Su rungumi noma da sauran ƙananan sana’o’i domin su dogara da kansu. Dogaro da kai shi ne asalin nasarar rayuwa. A haɗa ilimi da sana’a don amfaninsu,” in ji shi.