Fa’idojin dake tattare da cin dabino

1
373

Dabino yana ɗaya daga cikin ‘ya’yan itatuwa masu matuƙar amfani ga jikin ɗan Adam, saboda irin sinadaren da ya ɗauke dashi.

Dabino yana girma ne a bishiya kuma ‘ya’yan na cure ne kuma ya fi son yanayi mai zafi. Bayan ‘ya’yan dabinon sun nuna ana iya cinsu hakan nan kokuma a cire kwallon da ke ciki a sarrafa su ta wasu hanyoyin don more lagwada da amfanin da dabinon ke dauke dashi.

Ga dai wasu fa’idoji guda shida da dabino keyi a jikin dan adam;

1.Dabino nada tasiri wajen ƙara kuzari ga masu aure: Binciken masana kimiyyan sinadaren abinci ya nuna cewa dabino yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙara kuzari tsakanin ma’aurata.

Domin samun wannan fa’idar, sai mutum ya deɓi dabino kamar cikin hannunsa ya jiƙa su cikin nonon akuya su kwana, da safiya sai a markaɗa dabinon tare da nonon, kuma ana iya ƙara zuma da cardamom. Wannan haɗin yana da mutuƙar amfani wajen inganta kwanciyar aure.

2) Maganin gudawa: Dabinon da ya nuna sosai yana ɗauke da sinadarin potassium wanda ke da mutukar muhimmanci wajen magance gudawa.

Sinadarin fibre da ke cikin dabino kuma yana taimakawa wajen magance basir da sauran matsalolin da ke da alaka da fitar bayan gida da gyaran ciki.

3) Lafiyar zuciya: Dabino yana da matuƙar amfani wajen ƙarawa wa zuciyar dan adam lafiya. An fi samun fa’idan da ke cikin dabinon idan an tsoma shi cikin ruwa ya kwana sai a dauko a ci da safe. Hakan yana da matukar amfani ga masu fama da ciwon zuciya.

Sinadarin Potassium da ke cikin dabinon yana kare buguwar zuciya da wasu cututuka masu kama da hakan.

4)Ƙarin kuzari: Dabino na dauke da suga wanda basu da ila ga jikin dan adam kamar glucose, fructose da sucrose. Saboda hakan duk lokacin da mutum ke jin kasala idan yaci dabino zai samu kuzari nan take.

5) Ƙarfafa garkuwan jiki da magance allergy: Wani abin mamaki game da dabino shine yadda yake ɗauke da sinadarin sulphur wanda ba’a cika samunsa a ‘ya’yan itatuwa ba amma kuma yana da matuƙar amfani da jikin ɗan adam cikinsu kuwa harda ƙara karfin garkuwar jiki da magance ƙanana da manyan cututuka.

6) Yana taimakawa masu son mayar da jikinsu: Dabino na ɗauke da suga, sinadarin Protein da ke gina jiki da kuma vitamins. Kilogram daya da dabino na dauke da calories 3,000 wanda hakan sun isa jikin dan-adam biyan bukatun ta na kwana daya.Idan mutum ya rame kuma yana son mayar da kibansa, dabino na iya taimakawa wajen gina jiki sai mutum ya jibinci cin dabinon.

1 COMMENT

Leave a Reply