EFCC ta Kama Ɗan takarar Jam’iyyar NNPP a Kogi

2
780

Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati a Najeriya (EFCC) ta kama ɗan takarar Majalisar jiha na jam’iyyar NNPC a jihar Kogi, mai suna Ismaila Yusuf Atumeyi.

EFCC ta kama Ismaila Yusuf da tsabar kuɗi naira miliyan 326 da dalar Amurka dubu 140 da ɗari biyar.

An kama Ɗan takarar ne a Abuja a ranar Lahadi 30 ga watan Oktoban 2022 tare da ƙarin wasu da ake zargin da suka haɗar da Joshua Dominic wanda ake zargin shahararren ɗan damfara ne, sai Abdumalik Salau Femi, tsohon ma’aikacin banki wanda ake zargin shi ke bai wa ‘yan damfarar bayanai wajan satar kuɗi a asusun ajiyar bankin.

Hukumar ta kama tsohon ma’aikacin bankin ne a ranar Talata 1, ga watan Nuwamban 2022 a Legas, ta kuma gano tsabar kuɗi Dalar Amurka dubu 470 a gidansa.

Hukumar ta EFCC ta kwashe watanni tana binciken kafin ta kai ga kame waɗan ake zargin biyo bayan kutsen da suka yi a ɗaya daga cikin bankunan Najeriya inda suka saci kuɗi Naira biliyan ɗaya da miliyan dubu ɗari huɗu.

Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Ismaila Yusuf ya sami takarar kujerar ɗan najalisar jiha a jam’iyar NNPP inda yake fatan ya wakilci mazaɓar Anka 11 a jihar Kogi.

2 COMMENTS

Leave a Reply