Dokta Suleiman Shu’aibu Shinlafi Nagari Na Kowa

0
437

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

SAKAMAKON irin kokari da aiki tukuru wajen ganin ya inganta rayuwar al’umma a Jihar Zamfara mai ba Gwamna Shawara a kan harkokin hulda da kasashen waje Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya kara Daura dammarar ci gaba da kwazon aiki domin ganin tafiyar Gwamna Bello Muhammad Matawalle ta kara inganta ya sa Dokta Suleiman Shinkafi ya gayyaci dimbin al’umma domin su shaida abubuwan arzikin da ya kaiwa mutanen karamar hukumar Shinkafi.

Da farko dai kamar yadda wakilinmu ya ganewa idanunsa da kuma irin hotuna da bidiyon da ya gani na yadda Dokta Suleiman Shu’aibu Shinlafi ya halarci asibitin da ake kwantar da marasa lafiya inda ya rika raba masu tallafin kudi da kuma duba su a halin da suke ciki da yi masu gaisuwa bayan yin dubiya irin ta marasa lafiya, kai har ma da daukar jariran da aka haifa a wannan asibitin da ya kai ziyara tare da iyalansa.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya kuma tara wani babban taro a garin Shinkafi inda aka rabawa mata turamen zannuwa da sauran kayan amfani na yau da kullum domin tallafa masu kamar dai yadda aka san Dokta Suleiman S
Shinkafi da yin ayyukan jin kai.

Wannan kokari da jajircewar aikin ta Sanya wasu mutanen karamar hukumar Shinkafi suke yi wa Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi kirari sakamakon zama Gwarzon aiki da cewa “shalto kashe kwari”, ka yi taka ka yi ta mai karamin karfi fiya – fiya kashe kwari na Gwamnan Zamfara.

Wadansu kuma na cewa Inuwa baki kwamar kowa na Gwamna Matawalle a barka sai ta Allah ta yi, dukkan irin wadannan kalamai ne zaka ji mutane daban daban na fadi domin kawai su kwarzanta gwaninsu mai ba Gwamna Matawalle shawara a kan hulda da kasashen waje.

Za dai ku iya ganin hotunan dukkan abubuwan da muke gaya maku a cikin rubutun nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here