Daurarru a Gidan Yari dake Kano sun nemi tallafin Kayan Kwallon ƙafa

0
36
Daurarru a Gidan Yari dake Kano sun nemi tallafin Kayan Kwallon ƙafa

Daurarru a Gidan Yari dake Kano sun nemi tallafin Kayan Kwallon ƙafa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Daurarru a gidajen yarin Kano sun nemi tallafin kayan kwallo da suka haɗa da riguna, takalma, safa da ita kanta ƙwallon da za su riƙa amfani da ita wajen wasa.

Wannan na cikin wata hira da kakakin hukumar gidajen yari ta Kano, Malam Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, shine ya bayyana hakan yayin da yake sharhi kan wasan sada zumunta da aka buga tsakanin daurarrun da kungiyar ’yan Duniyar Bollywood.

KU KUMA KARANTA: Yan Daba sun shiga gidansu wani matashi sun kashe shi a Jihar Kano

Ya ce sun ji daɗi matuƙa da kulawar da kungiyar Duniyar Bollywood ta nuna, har ta zo gidan yari aka buga wasan kwallon kafa da su, wanda ya sanya farin ciki a zukatan daurarrun.

Malam Musbahu ya ƙara da cewa daurarrun na da sha’awar ci gaba da gudanar da irin waɗannan wasanni, amma suna fuskantar matsalar rashin kayan wasa.

Ya buƙaci alʼumma da ƙungiyoyi su ba da tallafin kaya sababbi ko tsofaffi domin ƙarawa ɗaurarrun ƙwarin gwiwa.

Gogaggen Dan Jaridar nan kuma jagoran magoya bayan India a Kano Muzammil Ibrahim Yakasai ne dai ya jagoranci wasan da aka buga tsakanin yan Bollywood da ɗaurarrun.

Leave a Reply