Dalilin da ya sa ‘ya’yana suka ƙi zabar sana’ar wasan kwaikwayo – Ali Nuhu

0
265

Shahararren jarumin fina-finan Kannywood da Nollywood, Ali Nuhu, ya ce ‘ya’yansa sun ƙi shiga harkar wasan kwaikwayo duk da sha’awar da ya ke dashi na su yi.

Tauraron fina-finan ya ce ɗansa, Ahmad mai shekaru 16 ya samu sha’awar wasan ƙwallon ƙafa yayin da ‘yarsa, Fatima ke da sha’awar karatun alaƙar ƙasa da ƙasa a jami’a.

Ali ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce yaransa biyu sun yi fice a sana’o’in da suka zaɓa.

“Gaskiya na fi son ɗana ya zama jarumi amma ya dage cewa yana da sha’awar ƙwallon ƙafa don haka na tallafa masa saboda a zamanin nan ba za ku iya tilasta wa yaranku sana’a ba.

“A matsayinka na uba idan ka gano sha’awar yaranka a kowace sana’a, dole ne ka ƙarfafa su. A gare ni, na fi son in yi aiki da shi amma ya dage kan wasan ƙwallon ƙafa.

KU KUMA KARANTA: Kasuwancin Hadin Gwiwa Na Bunkasa Tattalin Arziki – Sarkin Zazzau

“Fatima ta yanke shawarar ƙin yin wasan kwaikwayo tun tana shekara 13. Ta so ta karanci dangantakar ƙasa da ƙasa, kamar yadda nake magana tana gab da kammala matakin 300 kuma godiya ta tabbata ga Allah tare da ƙwarin gwiwarmu, tana cikin ɗaliban da ke da CGPA mafi girma a ajin ta.”

Dangane da yadda masana’antar fina-finan Hausa ke nunawa, jarumin ya ce an samu ci gaba, inda ya ƙara da cewa sana’ar na ci gaba da haɓaka cikin sauri, musamman ganin yadda Netflix da Amazon ke zuwa.

“Sana’ar tana ci gaba cikin sauri musamman ganin yadda Netflix da Amazon suka ɓullo a Najeriya kuma a can yanzu sun fi mayar da hankali kan fina-finan Hausa, ka ga idan a baya mun karaya mun daina shirya fina-finai, da ba mu cimma hakan ba. ” inji shi

Leave a Reply