Dalilin da ya sa ba a ga Gwamnan Kano a taron Gwamnonin arewa ba

0
38
Dalilin da ya sa ba a ga Gwamnan Kano a taron Gwamnonin arewa ba

Dalilin da ya sa ba a ga Gwamnan Kano a taron Gwamnonin arewa ba

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Babban Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Kano Malam Sunusi Sanusi Bature D-Tofa ya yi wa jaridar Neptune Prime hausa ƙarin bayani kan rashin ganin Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf a taron Gwamnonin Arewacin Najeriya da aka yi a Kaduna.

Ga karin bayaninsa:

Gwamnan Kano ya tura wakilcin Sakataren Gwamnati Alhaji Umar Faruk Ibrahim da Shugaban Ma’aikatan jihar Kano Abdullahi Musa don su wakilce a wancan taro.

Dalilin rashin zuwan Gwamna kuwa shi ne, tun a farkon shekara ya amince da jagorantar taron yaye dalibai da kafa gidauniyar tallafawa Jami’ar Kimiyya da fasaha ta Wudil wadda aka gayyato manyan attajirai domin su tallafawa jami’ar, irin su Alhaji Aliko Dangote wanda shi ne shugaban jami’ar, da abokinsa Otedola da kuma Alhaji Dahiru Barau Mangal da sauran su.

KU KUMA KARANTA:Gwamnonin Jihohin Arewa 19 da Sarakunan Gargajiya suyi taro a Kaduna

Babu yadda za a yi Gwamna ya tara wandannan baki su zo Kano domin fallafawa jiharsa kuma ya bar gari ya tafi taro.

Sannan babu dama ya tura mataimakinsa saboda shi ne Kwamashinan Ilimi Mai zurfi, dole akwai rawar da shi ma zai taka wajen wannan taro na jami’a.

Alhamdulillah, kwalliya ta biya kudin sabulu, domin a wajen wannan taro, an tarawa Jami’ar kudi da kayan aiki na sama da naira biliyan ashirin.

Leave a Reply